19 Yuli 2024 - 14:58
Kimanin Mutane Miliyan 6 Ne Suka Halarci Karbala Mu'alla A Taron Ashura

Ma’aikatar yada labarai da sadarwa ta kasar Iraki ta kuma sanar da cewa, 'yan jarida 725 da tashohin tauraron dan adam 84 ne suka dauki nauyin yada yadda aka gudanar da ziyarar Ashura a wannan shekara ta 1446 hijriyya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Majalisar lardin Karbala ta sanar a jiya Alhamis cewa kimanin maziyaarta miliyan shida daga kasar Iraki da wasu kasashe ne suka halarci taron Ashurar Imam Husain As da zaman makokin Tuwairij.

Kafin nan, ma'aikata, tsaro da kuma cibiyoyin lafiya sun sanar da nasarar shirin na musamman na taron Ashura da juyayi da makokin Taweerij.